RAHA A WASU WAQOQIN ALIYU NAMANGI

TSAKURE
Wannan bincike mai taken Raha a wasu Waqoqin Aliyu Namangi. Ya nazarci wasu waqoqin ne daga cikin waqoqin Aliyu Namangi waxanda ake hasashen cewa qunshe suke da zantuttuka na raha a cikinsu. Wannan bincike ya nuna cewa zantuttuka na raha na da matuqar muhimmanci a rayuwar al’umma musamman ma ga al’ummar Hausawa. Haka kuma binciken ya fahimci cewa wannan salo na yin amfani da zantuttukan raha a waqoqin Hausa kan haifar da nishaxuwa, da gundura yayin karantawa ko sauraron waqoqin. Sakamakon haka sai aka karkasa aikin zuwa babi-babi har guda biyar kamar haka: Babi na xaya ya kasance shimfixa ce da ke haskaka aikin baki xayansa. Babi na biyu kuwa ya waiwayi wasu ayyuka ne da suka gabata masu alaqa da wannan aikin. Babi na uku ya bayyana ire-iren hanyoyin da aka bi ne wajen tattaro bayanan da suka taimaka wajen gudanar da wannan binciken. A babi na huxu kuwa an bayyana wuraren da Aliyu Namangi ya sarrafa raha ce a wasu waqoqinsa. Wato kamar waqar Basukur da waqar zambon qazama da waqar Kuntugin Shaixan da waqar Tambihul Anami. Sai babi na biyar a inda aka naxe aikin gaba xayansa tare da bayar da wasu ‘yan shawarwari ga ‘yan uwa xalibai da kuma manazarta waqoqin Hausa.


ABSTRACT
This research work titled “Raha a wasu waqoqin Aliyu Namangi” (Comedy in some of Aliyu Namangi’s poems) comprises of explanations of how the Artist used comedic expressions in some of his poems. The work also made some criticisms on the kinds of comedic statements he used in the poems to entertain the people. At the end of the study, it was discovered that Aliyu Namangi used these statements in his poems in order to strenghten the relationship that exists between him and his relatives even though the poems were spiritual in nature.


BABI NA XAYA 
SHIMFIXA

1.0    Gabatarwa

Marubuta waqoqin Hausa wasu mutane ne da Allah (S.W.T) ya ba su wata baiwa da hikima da fasaha ga kuma basira wajen shirya waqoqin Hausa a rubuce, domin isar da wasu saqonni masu muhimmanci ga al’umma. Haka kuma sukan shirya waqa su kuma tsara ta a kan abubuwa daban-daban waxanda suka shafi rayuwar jama’a.

Har wa yau kuma kusan kowanne marubuci da irin hanya ko salon da yakan bi wajen tsara waqarsa, duk da cewa mafiya yawa daga marubuta waqoqin Hausa sukan rubuta waqoqinsu ne bisa jigon wa’azi da gargaxi da tarbiyya ko faxakarwa.

Haka kuma wani lokaci marubuta waqoqin Hausa kan yi amfani da wasu zavavvun kalmomi ko wasu zantuka na musamman a waqoqinsu domin samar da raha ko sanya nishaxi a zukatan jama’a saboda hakan zai haifar da rashin gundura ga mai karatu ko sauraron waqoqin Aliyu Namangi.

Aliyu Namangi na xaya daga cikin ire-iren waxannan marubuta waqoqin Hausa wanda ya yi amfani da wasu zavavvun zantuka na raha a wasu waqoqinsa, a inda wannan bincike zai gudana a kansu domin gano ire-iren rahar da ya yi amfani da su a waxannan waqoqin nasa da ake hasashen cewa suna qunshe da zantuka na raha a cikinsu.


1.1       Taqaitaccen Tarihin Aliyu Namangi

Fagen nazari na tarihin rayuwa da ayyukan marubuta waqoqin Hausa, fage ne mai faxi wanda masana da manazarta suka jima suna binciko tarihin xaixaikun
marubuta waqoqin Hausa da ayyukansu, domin bayar da gudummuwa tare da bunqasa wannan fage na adabin rubutacciyar waqa.

Masana da manazarta da dama sun kawo tarihin Aliyu Namangi a aikace-aikacensu da suka gudanar, ire-iren waxannan ayyuka na manazarta kan Aliyu Namangi sun haxa da Skinner (1969) da Xangambo (1973) da Hassan (1973) da Birniwa (1989) da Yakawada (1987) da Sankalawa (2005) da Muhammad (2010) da Muhammad (2011) da Nazifi (2011). Dukkansu sun bayyana cewa an haifi Aliyu Namangi ne a wani qauye mai suna Mangi a kusa da birnin Zariya. Hijira na da shekara dubu xaya da xari uku da goma sha biyar (1315) A.H. wacce ta yi dai-dai da shekara ta dubu xaya da xari takwas da casa’in da huxu (1894) A.D. A ranar Larabgana wato Larabar qarshen watan safar, wato watan biyu na Musulunci.

An kuma haife shi ne a lokacin sarkin Zazzau Kwasau, sunan mahaifinsa Ishaq, sunan mahaifiyarsa kuwa Hauwa’u. An haifi Aliyu Namangi lafiyarsa qalau kamar sauran jarirai. Bayan shekara xaya da haihuwarsa a watan safar sai idanunsa suka tsiyaye a sakamakon rubdugun cutar ‘qyanda’ da ta ‘Agana’ da suka same shi a lokaci xaya. Wannan shi ne musabbabin makancewar Aliyu Namangi, kuma an yi masa kaciya yana da shekara bakwai da haihuwa. (Yakawada, 1987:6-8).

For more Hausa Projects Click here
================================================================
Item Type: Project Material  |  Size: 112 pages  |  Chapters: 1-5
Format: MS Word  |  Delivery: Within 30Mins.
================================================================

Share:

No comments:

Post a Comment

Note: Only a member of this blog may post a comment.

Search for your topic here

See full list of Project Topics under your Department Here!

Featured Post

HOW TO WRITE A RESEARCH HYPOTHESIS

A hypothesis is a description of a pattern in nature or an explanation about some real-world phenomenon that can be tested through observ...

Popular Posts