MATSAYIN FASHI A {AGAGGUN LABARUN HAUSA

TSAKURE
Wannan binciken a fagen rubutun zube aka gudanar. Zube na ]aya daga cikin manyan rassan adabin zamani da suka ha]a da rubutacciyar wa}a rubutaccen wasan kwaikwayo. Binciken kan matsayin fashi ne a }agaggun labarun Hausa. An kawo ma’anar fashi an kuma bi diddigin asalin fashi a al’ummar Hausawa a gargajiyance. An yi tsokaci a kan shigowar zamani tare da nuna tasirinsa ta fuskar sauye-sauyen da aka samu a labarun da aka nazarta. A }arshen kowane labari da aka nazarta an bayyana sakamakon fashi ga al’ummar labarin da kuma sakamakon fashi a kan ‘yan fashin kowane labari ta fuskar irin hukuncin da aka yi masu.


ABSTRACT
The research discusses prose particularly; prose is a genre amidst other genres of Hausa modern literature that encompasses poetry and drama. The research examines position of robbery in three selected Hausa novels. The meaning of the word robbery (fashi) was fully explained and the origin of robbery (fashi) was traced from the Hausa traditional setting. The work has identified robbery as a phenomenon, but yet a traditional occupation in Hausa community which authors write novels among other phenomena that affects the society. This work studies three novels, identifies various manifestations of robbery and the technicalities employ in the execution of robbery including the types of arms used.


1.0       BABI NA [AYA:  GABATARWA

1.1       Shimfi]a

Wannan binciken an gudanar da shi ne a fagen rubutun zube. Zube reshe ne na adabin zamani cikin dangin rubutattun wa}o}i da rubutattun wasan kwaikwayo. Rubutun zube fage ne da marubuta }agaggun labaru ke rubuta labaru kan jigo iri-iri da suka shafi nau’o’in rayuwar al’umma don ilmantarwa da fa]akarwa da kuma nisha]antarwa. Marubuta sukan gina labarunsu kan jigon jaruntaka ko fita bi]a na aure ko na haihuwa ko kan wani sarki ko sarauniya da suka shahara wajen fa]in }asa, da iya mulki da tarin arziki ko kan wani hamsha}in mai arziki. Jigon kuma yana iya kasancewa kan wani gawurtaccen ~arawo ko gungun ’yan fashi da suka addabi }asa ko gari ko wata al’umma.

Fahimtar cewa marubuta labaru ba sa }wansu sai da zakara, hakan ya nuna cewa duk abin da suka wallafa a wasance ko a wa}yance ko a habarce yana nuna wani nau’i ne na hoton rayuwar al’ummar da aka wallafa labarin a kansu. Ashe kenan, ~arayi gawurtattu da mawallafa }agaggun labarun Hausa ke rubuta labaru a kansu, na nuna cewa shi halin ~arayin wani nau’i ne na rayuwar Hausawa, wannan halin kuwa kowa ya san shi wato sata. Sata kuwa kandamin suna ne da ya }unshi rassa irin su sane da yankan aljihu da }wace da }o}uwar sata wato fashi.Wannan bincike ya za~i ]aya daga cikin wannan rassa na sata wato fashi domin nazartar matsayinsa a wasu }agaggun labarun Hausa guda uku da suka ha]a da Idon Matambayi da Da’u Fataken Dare da kuma Za~i Naka. Taken binciken kuwa shine “Matsayin Fashi a Wasu {agaggun Labarun Hausa”.


1.2       Matsalolin Bincike

Babbar matsalar wannan binciken shi ne shi kansa batun da za a gudanar da binciken a kansa wato fashi. Daga jin kalmar fashi a kowacce irin al’umma ba ma sai an yi }arin bayani ba matsala ce babba domin hali ne mummuna na tashin hankali, wanda kowane addini ke }yamata. Wata matsalar ita ce waibuwar masu irin wannan nau’i na rayuwa, domin fuskantar su don jin }arin bayanin halayensu, domin fahimtar dalilan da suka yi tasiri har suka haifar da suke yin fashi da har ya ja hankalin mawallafa }agaggun labaru suke wallafa labaru a kai.1.3       Tambayoyin Bincike

Tambayoyi da ka iya tasowa lokacin gudanar da wannan bincike sun ha]a da fahimtar dalilan da ke sa ake }yamatar gudanar da bincike a kan irin wannan fage na fashi, duk da cewa ko an }i, ko an so, fashi nau’i ne na rayuwa da ana iya gudanar da bincike a kansa. Sannan za a fahimci shin wanne irin sakamako za a
samu a }arshen kowane }agaggen labari wanda aka nazarta? Shin wa]annan labarum sun gyara al’umma ne? ko kuma sun }ara ~ata al’umma ne? wa]annan irin tambayoyi za a sami amsoshinsu a }arshen wannan bincike.


1.4       Manufofin Bincike

An fahimci cewa gudanar da bincike a irin wannan nau’in rayuwa ba shi da farin jini. Wannan ba ya rasa nasaba da }yamatar halin saboda addini. Ga shi fashi ya zama nau’in rayuwar Hausawa wanda har ya ja hankalin mawallafa suna rubuta }agaggun labaru a kai. Wannan ne ya sa wannan binciken ya le}o fagen domin gudanar da bincike a kansa. Idan aka sami nasarar fito da fagen aka san sa, wata}ila a rage aikata halin, ko ma halin ya kau baki ]aya. Wata manufar kuma ita ce, ana fata in an amince da binciken, zai iya shiga jerin sababbin bincike da aka gudanar a sabon fage na adabin zamani. Kuma ana fata binciken ya zama abin kwatanci a ]akin karatu, domin masu bincike su waiwaya shi domin gudanar da wani binciken mai nasaba da wannan binciken. Ta fuskar iyaye da hukuma, mai yiwu wa suna iya fahimtar ha}}o}in da ke wuyansu na ‘ya’yayensu domin biya musu bu}atunsu. [an fashi shi ne }ololuwan |arawo a hali na sata. In kuwa tun daga gidaje yara an biya musu bu}atunsu to ba za su koyi ‘yar sace-sace ba.


1.5       Farfajiyar Bincike

Kowane irin aiki yana bu}atar kadada ko iyaka. Wannan binciken ya duba matsayin fashi ne a rayuwar Hausawa inda aka nazarci wa]ansu }agaggun labarun Hausa guda uku mabambanta lokaci da shekaru. Labarun su ne Idon Matambayi na Muhammadu Gwarzo 1934 da Da’u Fataken Dare na Tanko Zango da aka buga 1978 da Za~i Naka na Munnir Muhammed Katsina 1982. An yi bayani kan ma’anar kalmar fashi da asalin fashi shi kansa, an kuma kawo fasalce-fasalcen fashi a gargajiyance tare da yin bayani kan yadda zamani ya yi tasiri akan harkar fashi a jerin labarum uku. A }arshe sai aka kawo sakamakon fashi da ]an fashi a kowane labari cikin binciken.


1.6       Hanyoyin Gudanar da Bincike

Hanyoyin da aka bi domin samun bayanai don gudanar da wannan binciken sun ha]a da:

a.   Karatu don nazarin wasu }agaggun labarum Hausa da aka za~a domin gudanar da wannan binciken da ma wasu labarun }agaggu na Hausa masu nasaba ta kusa, da masu nasaba ta nesa da wannan binciken.


b.   Hira tare da tattaunawa da ]aya daga cikin mawallafa labarun.(Munnir Muhammad Katsina) mawallafin Za~i Naka domin jin wa}a daga bakin mai ita.

c.       Hira tare da tattaunawa da kuma neman shawarwari a wajen masana da manazarta adabin zamani da kuma masu sha’awar adabin zamani a jami’o’i da sauran makarantu na ilmi.

d.      Nazarin kundayen digiri da mu}aloli da mujallu masu ala}a da wannan binciken komai }an}antar ala}ar.

e.       Hira ta kai tsaye da mahukunta wannan ]abi’ar na da da na yanzu. An yi hakan don ilmantuwa da irin hukunce-hukuncen da ake yi wa ‘yan fashi a da da kuma yanzu don kwatanci.1.7       Na]ewa

A babin an yi shimfi]a ce kan binciken ]ungurungun. A shimfi]ar an nuna cewa a rubutun zube aka gudanar da binciken. An kawo dangin zube wato rubutattun wa}o}i da rubutattun wasan kwaikwayo duk }ar}ashin adabin zamani suke. An kawo ire-iren nau’o’in jigogin da marubuta ke rubuta labarunsu a kai. An nuna a babin cewa sata nau’i ne na rayuwa, an kawo rassan sata da su ka ha]a da fashi. An nuna cewa a kan jigon fashi aka gudanar da wannan binciken. An bayyana cewa an nazarci matsayin fashi ne a wasu }agaggun labarum Hausa. An
kawo sunayen labarun da aka nazarta. Sannan sai tsokaci da aka yi na matsalolin binciken da tambayoyin binciken da manufofin binciken da farfajiyar binciken da kuma hanyoyin da aka bi don gudanar da binciken.

For more Hausa Projects Click here
================================================================
Item Type: Project Material  |  Size: 168 pages  |  Chapters: 1-5
Format: MS Word  |  Delivery: Within 30Mins.
================================================================

Share:

No comments:

Post a Comment

Note: Only a member of this blog may post a comment.

Search for your topic here

See full list of Project Topics under your Department Here!

Featured Post

HOW TO WRITE A RESEARCH HYPOTHESIS

A hypothesis is a description of a pattern in nature or an explanation about some real-world phenomenon that can be tested through observ...

Popular Posts