KWAMACALA A RUBUTUN HAUSA: NAZARI A KAN RUBUTUN LITTATTAFAI DA JARIDU DA MUJALLU DA ALLUNAN TALLA DA ABUBUWAN HAWA

TSAKURE
Ganin halin da rubutun Hausa yake ciki na ci gaba da qara bunqasa a wannan lokaci da kuma irin kwamacalar da ake samu wajen amfani da shi, musamman a jaridu da mujallu da allunan talla da ma littattafai da sauran fannoni na rayuwa, ya sanya wannan bincike ya yi nazarin wannan al’amari da nufin fito da irin matsalolin da ake fuskanta a yayin gudanar da rubutuun Hausa.
Su kuwa waxancan hanyoyin samar da bayanai da aka yi nazarin su, sun zama abubuwa ne da ake amfani da su a yau da kullum, musamman ga waxanda suka samu damar yin ilimin karatu da rubutu na boko. Don haka ne wannan bincike ya waiwayi yadda ake amfani da rubutun Hausa a cikinsu da irin kurakuran da ake samu a yayin yin rubutu.

BABI NA XAYA 
GABATARWA

1.0       Gabatarwa

An daxe ana gabatar da nazari a kan jaridu da mujallun Hausa kama tun daga tarihin samuwarsu da yadda suke amfani da harshe a fagen sadarwa da irin salon da suke amfani da shi da muhimmancinsu ga al’umma da ire-irensu ta fuskar bayanan da suke qunshe da su,

Dalilin gudanar da wannan bincike shi ne domin sanin halin da rubutun Hausa yake a cikin littattafai da jaridu da mujallu da allunan talla da jikin abubuwan hawa da ma sauran wurare da ake amfani da shi, tare da yin nazarin irin matsalolin da ake fuskanta a fagen rubutu a waxannan kafafen ilmantarwa da wayar da kan al’umma.

1.2       Manufar Bincike

Manufar wannan bincike ita ce, yin zuzzurfan bincike a kan yadda jaridu da mujallu da allunan talla suke gudanar da rubutun Hausa, musamman ta amfani da qa’idojinsa, kuma an yi nazarin irin kurakuran da ake samu a yayin rubuce-rubucen tare kuma da gano hanyoyin da za a kauce musu da kuma bayar da shawarwarin yadda za a inganta rubutun Hausa.

1.3       Dalilin Bincike

Ganin irin muhimmancin da rubutu yake da shi da kuma dangantakar da ke tsakanin rubutu da kafafen isar da saqo na jaridu da mujallu da allunan talla ya sa wannan bincike ya yi nazarin irin yadda ake gabatar da rubutuna waxannan kafafe da nufin gano ire-iren matsalolin da ake samu.

1.4       Muhimmancin Bincike

Babban muhimmancin wannan bincike shi ne taimaka wa masu amfani da rubutun Hausa domin samun isar da saqo cikin sauqi ba tare da sauyawa ko salwantar ma’ana ba. Akwai fannoni da dama da ake amfani da rubutun Hausa; ta fuskar ilimi zai taimaka wajen fahimtar irin kurakuran da ake samu a yayin gudanar da rubutun Hausa. Haka nan zai taimaka wajen fahimtar da al’uma cewar ba duk mai iya karatu da rubutu ba ne zai iya rubutu da Hausa a bias qa’idojinta, don haka akwai buqatar samun ilimin qa’idojin rubutu na Hausa. Haka nan zai taimaka wa kamfanoni masu yin tallace-tallace a rubuce su fahimci cewar suna kasha maqudan guxaxe ta wannan fuskar, amma kwalliya bat a biyan kuxin sabulu domin kuwa a mafi yawanci lokuta ba saqon da suke son a isar ake isarwa ba, a wani lokaci ma babu ma’ana ga abin da ake rubutawar. Irin wannan matsala tana faruwa a tallar da ake yi a jaridu da mujallu da kuma allunan talla.

1.5       Hanyoyin Gudanar da Bincike

Yayin gudanar da wannan bincike an karanta jaridu da mujallu da nazarin allunan talla da rubuce-rubuce a jikin abubuwan hawa, musamman motocin haya da nufin zaqulo kurakuran da ake samu. Don haka akwai buqatar a kalle su, a xaixaikunsu. Saboda haka hanyoyin da aka bi wajen gudanar da wannan bincike sun haxa da:

Karanta littattafai, musamman masu magana a kan qa’idojin rubutu na Hausa da jaridu da mujallu, don yin nazarin yadda ake gudanar da rubutun Hausa a cikinsu. An kuma yi nazarin kundayen binciken digiri na biyu da na uku da aka gudanar a kan rubutun Hausa ko a kan littattafai da jaridu da mujallun Hausa don samun qarin haske a kan hanyoyin da aka gudanar da wannan bincike. An kuma gana da masana da editoci da ‘yan jarida da masu karanta jarida da karanta littattafai da suka danganci rubutun Hausa da masu bayanai a kan jaridu da mujallu. Sannan kuma an karanta kuma aka juyi wuraren da aka yi kurakurai don nazartar su.

Haka kuma an ziyarci xakunan karatu na jami’o’i, musamman na jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya da jami’ar Bayero da ke Kano da jami’ar Usmanu Xanfodiyo da ke Sakkwato da kuma jami’ar Umaru Musa ‘Yar’aduwa da ke Katsina domin yin nazarin bayanai da suka shafi qa’idojin rubutu na Hausa da kuma yadda ake amfani da su a rubuce-rubuce na yau da kullum.

1.6       Farfajiyar Bincike

Wannan bincike ya gano ire-iren matsalolin da ake samu a rubuce-rubucen da ake yi a cikin littattafai da jaridu da mujallu da allunan talla da jikin abubuwan hawa da sauran hanyoyin sanarwa a rubuce. Ta vangaren jaridu aikin ya yi nazarin Jaridar Gamzaki da Jaridar Leadership Hausa da At-tatbiq da Aminiya da Gaskiya Ta Fi Kwabo da kuma Jaridar Rariya. A vangaren mujallu an yi nazarin Mujallar Fim da Xakin Kara da Mujallar Gani da Ido (Maganin Tambaya) da Mujallar Kulawa da Mujallar Magama da Kunnen Gari, (in ka ji, kowa ya ji) da Mujallar Sautus Sunnah da kuma Muryar Arewa,

Haka nan binciken ya yi nazari a kan rubutu na Hausa a yau; yadda suke da yadda ake gabatar da su. Haka nan wannan aiki bai taqaita ga wani vangare na qasar Hausa ba, musamman ganin abubuwan hawan da aka yi nazari suna yin zurga-zurgarsu ne a duk faxin garuruwan qasar Hausa.

Aikin kuma ya yi nazarin rubutun Hausa a kan tituna, wato yadda ake amfani da shi don yin sanarwa ko gargaxi ko tallace-tallace a jikin bangaye ko qananan allunan talla ko na sanarwa (sign boards)

1.7       Hasashen Bincike

Hasashen wannan bincike dai shi ne dalilan da suke haddasa kwamacala a rubutun Hausa guda biyu ne; na farko shi ne take sani, musamman inda ake samun masu ilimi suna yin rubutun Hausa ba bisa qa’ida ba. Wannan ba ya rasa nasaba da halin Bahaushe na ‘shakulatin vangaro’ wato ko in kula ga abin da ya wajaba a yi wato dai an wallafa littafi don wata manufa, amma an qi kulawa tare da tabbatar da an cim ma wannan manufar. Wannan ne yakan sanya a samu kura-kurai a cikin litattafai da aka wallafa su don su zama jagora ga mai rubutun Hausa, watoya zama mai dokar barci yana gyangyaxi.

Dalili na biyu kuwa shi ne na rashin sani a game da rubutun Hausa bare kuma qa’idojinsa. Irin wannan matsala ita ce ta fi shafar masu rubuce-rubuce a jikin abubuwan hawa da katin gayyata da sanarwa ko gargaxi da ake samu a wurare daban-daban. Buqatar irin waxannan marubuta dai ita ce ta isar da saqon da ake tunanin an isar ko ta halin qaqa.

1.8       Naxewa

Wannan bincike ya mayar da hankali ne a kan kwamacalar da ake samu a rubutun Hausa a littattafai, musamman masu bayani a kan qa’idojin rubutu da jaridu da mujallu da jikin abubuwan hawa, musamman motocin haya da allunan talla da sauransu da nufin zaqulo irin kurakuran da ake samu da kuma yin cikakken tsokaci a kan kowace qa’ida aka kawo da abin da ya faru har ake ganin an sava wa waxannan qa’idoji.

For more Hausa Projects Click here
================================================================
Item Type: Project Material  |  Size: 134 pages  |  Chapters: 1-5
Format: MS Word  |  Delivery: Within 30Mins.
================================================================

Share:

No comments:

Post a Comment

Note: Only a member of this blog may post a comment.

Search for your topic here

See full list of Project Topics under your Department Here!

Featured Post

HOW TO WRITE A RESEARCH HYPOTHESIS

A hypothesis is a description of a pattern in nature or an explanation about some real-world phenomenon that can be tested through observ...

Popular Posts