HA[EJANTATTUN KALMOMI DA ZANTUKA NA MUSAMMAN

GABATARWA

Wannan aiki mai taken ‘Ha]ejantattun Kalmomi Da Zantuka Na Musamman’, kamar yadda sunan ya nuna, aikin ya dogara ne kan kalmomi da zantuka waxanda suka ke~anta ga karin harshen Ha]ejanci. An kasa wannan aiki zuwa gida biyar. Kowane kashi babi ne mai zaman kansa. A babi na xaya gabatarwa ce ta aikin baki xaya, a cikin babin an kawo bitar ayyukan da suka gabata da dalilin bincike da muhimmancin bincike da hanyoyin gudanar da bincike da faxin bincike sannan naxewa. A babi na biyu, an gabatar da bayanai a kan ma’anar harshe da ma’anar karin harshe da rabe-raben karin harshe da kuma dalilan da suka haifar da karin harshe sannan naxewa. A babi na uku an kawo bayanai a kan mene ne Haxejanci da su waye Haxejawa da ina ne Haxeja da kuma Haxejantattun kalmomi da suka shafi zantukan yau da kullum da waxanda suka shafi sassan jikin xan Adam da waxanda suka shafi dabbobi da tsuntsaye da waxanda suka shafi abinci da waxanda suka shafi abubuwa na yau da kullum da waxanda suka shafi sarauta da kuma waxanda suka shafi sunayen mutane, sannan aka naxe babin. Babi na huxu ya kawo bayani a kan nau’o’in jimlolin Hausa kamar sassauqar jimlar Hausa da jimlar korewa da jimlar tambaya da kuma jimlar umarni, daga nan sai aka naxe babin. Sai kuma babi na biyar wanda a cikinsa aka kammala aikin gaba xayansa. A qarshe gaba xaya an kowa manazarta sannan rataye.


{UMSHIYA

TAKE
GABATARWA

BABI NA [AYA
1.0       Shimfi]a
1.1       Bitar Ayyukan Da Suka Gabata
1.2       Dalilin Bincike
1.3       MuhimmancinBincike
1.4       Hanyoyin Gudanar Da Bincike
1.5       Faxin Bincike
1.6       Na]ewa

BABI NA BIYU
2.0       Shimfi]a
2.1       Ma’anar Harshe
2.2       Ma’anar Karin Harshe
2.3       Rabe-raben Karin Harshe n Hausa
2.4       Dalilan Da Suka Haifar Da Rabe-raben Karin Harshen Hausa
2.5       Naxewa

BABI NA UKU
3.0       Shimfi]a
3.1       Mene Ne Ha]ejanci?
3.2       Su Waye Ha]ejawa?
3.3       Ina Ne Ha]eja?
3.4       Ha]ejantattun Kalmomi Da Suka Shafi Zance Na Yau Da Kullum
3.5       Ha]ejantattun Kalmomi Da Suka Shafi Sassan Jikin [an Adam
3.6       Ha]ejantattun Kalmomi Da Suka Shafi Dabbobi Da Tsuntsaye
3.7       Ha]ejantattun Kalmomi          Da Suka Shafi Abinci
3.8       Ha]ejantattun Kalmomi Da Suka Shafi Abubuwa Na Amfanin Yau Da Kullum
3.9       Ha]ejantattun Kalmomi Da Suka Shafi Sarauta
3.10     Ha]ejantattun Kalmomi Da Suka Shafi Sunayen Mutane
3.11     Na]ewa

BABI NA HU[U
4.0       Shimfi]a
4.1       Sassauqar Jimlar Hausa
4.2       Jimlar Korewa
4.3       Jimlar Tambaya
4.4       Jimlar Umarni
4.5       Na]ewa
KAMMALAWA
MANAZARTA
RATAYE


ABI NA XAYA


1.0       Shimfixa

A wannan babi na farko an yi gabatar muhimman da abubuwan da suka shafi wannan bincike, kamar; dalilin yin bincike da muhimmancin bincike da hanyoyin gudanar da bincike da bitar ayyukan da suka gabata da kuma faxin aikin. Don haka, waxannan abubuwa da muka ambata, su ne za mu gani a wannan babin na farko, mai suna gabatarwa.

1.1       Bitar A yyukan Da Suka Gabata

An gudanar da ayyuka da dama a kan nazarin karin harshen Hausa. Wasu ayyuka an gudanar da su ne a matsayin wallafaffun littattafai, wasu kundayen bincike ne, wasu kuma maqalu ne. Daga cikin ayyukan da na yi bita sun haxa da:


Abdulqadir (1982) ta rubuta kundinta ne a kan karin harshen Sakkwato da karin harshen Kano. Ta raba aikin zuwa babi uku, ba da gabatarwa ba. A babi na farko ta yi bayani ne kan furuci, inda Sakkwatanci ya bambanta da Kananci. Alal misali, yadda Sakkwatanci ke levantar da saututtukan dasashi (labialization of alveolar sounds), da akasin haka a Kananci. A babi na biyu ta yi magana a kan yadda ake samun bambanci....

For more Hausa Projects Click here
================================================================
Item Type: Project Material  |  Size: 58 pages  |  Chapters: 1-5
Format: MS Word   Delivery: Within 30Mins.
================================================================

Share:

No comments:

Post a Comment

Note: Only a member of this blog may post a comment.

Search for your topic here

See full list of Project Topics under your Department Here!

Featured Post

HOW TO WRITE A RESEARCH HYPOTHESIS

A hypothesis is a description of a pattern in nature or an explanation about some real-world phenomenon that can be tested through observ...

Popular Posts